hausa.premiumtimesng.com
Kungiyar ‘Amnesty’ ta nemi Najeriya ta buga sakamakon zargin cin zarafin jama’a da sojoji ke yi - Premium Times Hausa
Kungiyar jin kai ta duniya, da aka fi sani da ‘Amnesty International’, ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da fitar da rahoton da kwamitin da shugaban kasa ya kafa a kan binciken zargin take hakkin jama’a da sojoji ke yi.